AdSense

Fayose Ya Karaya Da Takarar Shugabacin Najeriya

Gwamnan jijar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyan dalilan da suka sanya ya janye daga hankokinn neman shugabancin kasar nan a shekarar 2019.

Gwamnan mai barin gado ya yi wannan bayanan ne a garin Ado Ekiti ranar Juma’a, yayin da yake karbar bakoncin dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso, wanda ya isa jihar don neman goyon bayan wakilan jam’iyyar daga jihar a taron fida gwamna na jam’iyyar da ake shirin gudanarwa kwanan nan.

“A matsayi na shugaba na kwarai bai yi wu na bar mataimaki na da jam’iyyar APC ta kwace wa mulki zuwa neman wani matsayi ba,” inji Mista Fayose. “Postan da na buga  na cikin daki na iyana abin dake gaba na a  yanzu shi ne kokarin kwato mulkin da aka kwace mana.” A watan Satumba 2017 ne Mista Fayose ya aiyyana kudurinsa na takarar shugabancin kasar nan a wani taro a Abuja, in da ya yi alfaharin cewa, lallai ba abin da zai hana shi zama shugaban kasar nan a zaben shekarar 2019.

Ya kuma sha alwashin kada shugaba Buhari a zaben da za a gudanar. “Na gaiyato ku ne a yau, shugabanin jami’yyarmu don in sanar da ku cewa, zan tsaya takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, ina wannan ne don tabbata da ci gaban jam’iyyarmu.

 



No comments

Powered by Blogger.