Jirgin Kasan Kaduna-Abuja ya murkushe shanaye 53
Kwamishinan yan sandan jahar Kaduna ya tabbatar da mutuwar shanaye 53 a sanadiyar murkushe su da jirgin kasan Kaduna-Abuja yayi
Kwanishinan yan sanda Ahmad Abdurahaman yace hadarin ya faru ne a Kasarami cikin karamar hukumar Kagarko ta jahar Kaduna
A inda yace, an sanar dashi labarin hadarin ne ta wayar salula, hakan ya sa ya jagoranci tawagar yan sanda har zuwa wajen da hadarin ya afku
An samu gurguwar fahimta ne tsakanin makiyaya da wadanda suka tambaya cewar idan jirgi yana wuce wa a wannan rana ta Lahadi kuma a dai-dai wannan lokacin an basu amsa da cewa baya bin hanyar a yau, sai da suka hau titin na jirgin sunyi nisa sannan jirgin kasan ya taho daga tashar Rigasa kan hanyar zuwa Abuja, jirgin kasan na gudu sosai hakan yasa jirgin kasan ya murkushe shanayen har suka kai ga mutuwa sai dai 27 daga ciki na da sauran lumfashi haka yasa aka yanka su domin rage asara.
Kwamishinnan ya tabbatar wa da mutanen Kaduna cewa kaddara ce ta afkawa shanun amman ko mutum daya bai rasa ransa ba a irin hadarin da jirgin yayi.
Kwamishin yan sandan ya kara da cewa makiyayan na kan hanyar su ta tafiya Katsina ne hadarin ya afku sakamokon haka ne yasa ya gana da shugaban na makiyayan da kuma na manoman don yin bincike a gaba,
Kuma yayi kira ga mutanen Kaduna da su cigaba ayyukan su na alkairi sakamon ma’aikatan na kokarin ganin sun cigaba da kare dukiyoyin da rayukan al’ummar jahar baki daya.
No comments