APC Na Tsoran Tsayawa Ta Takarar – Bukola Saraki
Jam’iyyar APC na maraba da tsayawar shugaban majalisar dattijai sanata Bukola Saraki da tsayawar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP
Sai dai APCn na gargadin shi da cewa yan Najeriya fa sun gajiya da salon siyasar sa
Yayin da Saraki ya mayar da martani wajen cewa shugabanin na shakkar sa a matsayin wanda zai iya tsayawa takarar shugaban kasa kuma hakan ba zai razana shi ba
Sakataren yada labaran jam’iyyar AP,C Yekini Nabena, yayi Magana akan ayyuka dake a yankin na Saraki da yayi akai
Sai dai kuma Saraki yace shin ina ruwan APC da wata jam’iyyar ko yan takarar ta
ya kuma kara da cewa a bangaren nashi babu wata matsala sai idan shugabannin na jam’iyyar APC na son kirkirar wata matsalar
No comments