PDP Ta Yanke Shawarar tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa
Kwamitin amintattun jam’iyyar PDP ta kafa kwamiti don samar da mafita wajen fidda dan takarar shugaban kasa a 2019.
Kwamitin ya gargadi ‘ya ‘yan jam’iyyar da kada aci zarafin ko nuna kalaman aibu ga abokin takara da sunan yakin neman zabe
Shugaban Kwamitin amintattun, Walid Jibrin, yace, an yanke shawarar hakan ne bayan tattauna da kwamitoci da akayi, a ofishin dake Abuja a daran Lahadi
Walid wanda ya tattauna da yan jarida yace, kwamitin ya shirya tsaf don tattaunawa da ‘yan takarkarun don samar da masalaha wajan fitar da gwanin jam’iyar
Ya kara da cewa, an karawa shugabannin kwamitocin amintattun Karin shekara biyar
No comments