AdSense

Zaben Ekiti: Aminat Zakari Ta Nemi Fayose Da Ya Nemi Afuwarsu

Kwamishiniyar zabe ta Jihar Ekiti, Uwargida Aminat Zakari, ta bai wa Gwamnan Jihar Ekita awanni 48 da ya ba ta hakuri a bainar jama’a kan zarginta da ya yi da yi wa dan takarar Jam’iyyar APC Dakta Kayode Fayemi, aikin murguda zaben gwamnan Jihar a ranar Asabar.

A ranar 2 ga watan Yuli ne Fayose ya zargi ‘yan sanda da kuma sashen jami’an tsaro na DSS da tura jami’an tsaron da suke tare da Fayemi aiki a Jihar domin su shirya yadda za su murguda zaben Jihar. Hakanan gwamnan ya zargi Aishat Zakari da kuma wasu jami’an hukumar zaben uku Mista Kenneth Ukeagu, Abdulrazak Yusuf da Mista Abdulrasak Agboola, wanda ya ce duk suna aiki ne tare da Fayemi domin murguda zaben. Sai da take mayar da martani kan zargin na gwamnan ta hannun Lauyoyinta, ‘Ubong Akpan Chambers, Zakari cewa ta yi, wannan irin karyar mai zubar da mutunci ta shafi lafiyarta, aikinta, da rayuwar iyalanta.

Cikin karar mai taken, “Bayanan zubar da mutunci ga mutumiyar kirki kuma ma’aikaciya, Uwargida Amina Bala Zakari,’ wacce aka mika ta ga gwamnan, Lauyoyin Kwamishiniyar zaben sun bayyana cewa, “Kai (Fayose) Kirista ne kuma mai iyali tun kafin ka zama dan siyasa ko gwamnan Jihar Ekiti.

“Bai kamata ka yi zaton ko ta wane hali indai ba daman da gangan aka yi nufi ba, wani gwamna zai yi irin wannan zargin mai zubar da kima da mutunci ga wacce ta kasance, Uwa, Matar Aure, kuma ‘Yar’uwa a adamtaka, ya yi mata irin wannan mummunan kwatancin ba. “Karin bacin lamarin ma shi ne karyar da ta shafi zub da mutuncin da ka yi wa wacce muke wakilta a aikinta na al’umma.” Amina Zakari, tana bukatar Fayose ya rubuta ban hakuri ne a cikin manyan jaridun kasarnan duka a cikin awanni 48.

Zaben Ekiti: Kwamishiniyar Zabe Ta Nemi Fayose Da Ya Nemi Afuwarsu



No comments

Powered by Blogger.