AdSense

Naira Biliyan 242 Zata Kare A Zaben 2019 -Buhari

A ranar Talata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar kasa ta amince da kashe Naira Biliyan 242 don harkokin da suka shafi zaben shekarar 2019 da hukumar INEC za ta gudanar daga kudaden da suka sanya a cikin kasafin kudin.

A wasikar da shugaban kasar ya aikawa shugaban majalisar datijjai Bukola Saraki, aka kuma karanta a zauren majalisar ranar Talata, shugaban kasar ya ce, ‘yan majalisar na iya zaftare Naira Biliyan 578 daga cikin kudaden da a ka ware wa hukumar zaben tun da farko a cikin kasafin kudin shekarar 2018. A lokacin da shugaban kasar ke sanya hannu a kasafin kudin kwanaki ya jawo hankalin ‘yan majalisan da yadda suka yi gaban kansu na kara Naira Biliyan 578 a cikin kasafin kudin. Wasikar na bukatar majalisar kasar ne ta amince da kusan rabin kudaden da aka shirya z a a kashe tunda farko da kuma bukatar a kara wasu rabin kudaden don sabbin aiyyuka, aiyyukan da aka zayyana a matsayin masu mahimmanci gaske.

Shugaban kasa Buhari na bukatar majalisar kasar ne ta samar wa da hukmar INEC kudi Naira Biliyan 164.10 daga cikin kudaden da suka saka a cikin kasafin kudin da ake ganin ya kai fiye da Naira 578, a cikin Naira Biliyan 78.340 da ake bukatar don fuskantar zaben shekarar 2019 kamar dai yadda a ka tanada a cikin kasafin kudin shekarar 2019. Ana ganin wannan lamarin zai iya sake tayar da jijiyar wuya tsakanin majalisar kasar da fadar shugaban kasa saboda tunda farko ‘yan majalisar sun bayyana cewa karin da suka yi a kasafin kudin shekarar 2018 ya faru sakamako karuwar da aka samu na kudin gangan man fetur a kasuwanni duniya da kuma bukatar a rarraba aiyyukan gwamnatin tarayya ga sassan kasa baki daya ba wai a cunkusa aiyuukan a yanki daya ba. A wasikar da aike wa majalisar ranar Talata, Shugaba buhari ya na bukatar ‘yan majalisar ne dasu amince da Naira Biliyan 242 don harkokin da suka shafi zaben shekarar 2019.

Wasikar shugaban kasar ta kuma bayyana cewar, ‘yan majalisar su dauko daga cikin Naira Billiyan 242, 445, 322, 600.00 na harkokin zaben shekarar 2019, sai su ciro Naira Biliyan 164.104 daga cikin da aka ware wa majalisar kasa ta kudaden da ‘yan majalisar sika soka cikin kasafin kudaden, sannan abin daya rage na Naira Biliyan 78.340 sai a samar dasu daga cikin kasafin kudin shekara mai zuwa na 2019. Wasikar ta kuma ce, shugaban kasa na bukatar a ciro Naira Biliyan 228, 864, 008 da Naira Biliyan 215  daga cikin kudaden da ‘yan majalisa suka sako a cikin kasafin kudin, da kuma naira Biliyan 578 da suka sanya a cikin Naira Triliyan9.12 daga cikin kudaden da majalisar kasa ta aiyyana kashe a kasafin kudin shekarar 2018. Wasikar shugaban kasar ta kuma ci gaba da cewa, “Kudaden da ake bukata kamar yadda muka sanya a kasafin kudin shekarar 2018 domin gudanar da zaben shekarar 2019 da kuma farfado da aiyyanannun aiyyuka shi ne Naira Biliyan 228,854,008,215.

“Aiwatar da kasafin kudi na naira Tiriliyan 9.12 a shekarar 2018 zai yi matukar tsauri, saboda haka bazan yarda da kara wasu kudade ba domin kara wasu kudade a kasafin shekarar 2018 domin gudanar muhimman aiyyuka a shekarar 2018. “A saboda haka ina gaiyyatar ‘yan majalisar dattijai das u dubi yanayin da kasa take ciki su gaggauta samar da wadanna kudaen daga kudin da suka sako dashi a cikin kasafin kudaden na shekarar 2018 wadda gaba daya kudaden ya kai Naira Biliyan 578,319,951,904 domin a yam aye gurbin naira 228,854,008,215 kamar yadda ake bukata muka kuma nusar a sama.”

A cikin wasikar, shugaban kasa ya yi bayanain cewa, ana tsananin bukatarb Naira Biliyan 164 cikin gaggawa don gudanar da harkokin zaben shekarar 2019, kamar haka, Hukumar Zabe INEC, Naira Biliyan 43,512,529,455.00 sai ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro (NSA) aira Biliyan N3,855,500,000 da kuma ofishi DSS Naira 2,903,638,000 sai hukumar NSCDC Naira 1,845,597,000 hukumar ‘yan sanda kuma Naira 11,457,417,432 yayin da ake bukatar Naira Biliyan 530 ga hukumar NIS.



No comments

Powered by Blogger.