Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayyya Ta Saki Dasuki
Babbar kotun tarayya wadda tayi zamanta a Abuja daga karshe dai ta bada takarda, wadda bukatar shugaban Hukumar tsaro ta farin kaya, da kuma Antoni janar da tarayya, kuma Ministan shari’a cewar su bada belin Sambo Dasuki.
Ranar 2 ga watan Yuli na wannan shekara da misalin karfe daya , ita kotun ta bada belin Mr Dasuki duk ya cika su. PR Najeriya ta samu bayanin cewar da misalin karfe daya ne ranar Talata mai bada belin kotun da kuma wasu mutane biyu da suka tsaya ma shi, suka shi shugaban Hukumar tsaro ta farin kaya da kuma shi Ministan shari’a kuma Antoni janar na tarayya takarda daga babbar kotun tarayya, wadda ta bada umarnin a bada belin.
Koda yake dais u wadanda suka tsaya ma shi suna sa ran zasu tafi tare da tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa, amma kuma suna ganin shi shugaban Hukumar DSS, yana bukatar da ya tuntubi fadar shugaban kasa, kafinn ya kai ga mika Dasuki gare su, saboda abi umarnin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta bada dangane da hakan.
Ita dai takardar umarnin da a sake shi din tana dauke da ranar 16 ga watan Yuli, an kuma yi mata taken ‘’ Tabbatar da sharuddan bada beli’’ da kuma dauke da sa hannun Mba Nkem wanda shi ne mataimakin Rajistara, an kai ma hedikwatar DSS da kuma ofishin Ministan shari’a. Takardar bada umarnin da a saki wanda ake tsaren da shi, ita ce kamar haka ‘’ Dalilin da hukuncin da aka yanke na ranar Litinin 2 ga watan Yuli 2018, wanda mai shari’a Hon Justice Ijeoma L. Ojukwu, wadda ta bayyanan sharuddan da za a cika su, kafin a bada umarni bada belin, kamar yadda aka bukata, na (Ritayar Sambo Dasuki). ‘’ Na tabbatar da dukkan sharuddan, kamar dai yadda aka bukata, da kuma wasu abubuwa uku da sai an yi su tukuna. ‘’ Su wadanda ya dace a sanar dasu kamar shugaban Hukumar tsaro ta farin kaya, da kuma Antoni janar na tarayya da cewar su bai shi umarnin.
‘’Wadannan takardun kuma umarni ne daga ita kotunb dam kuma duk wadansu takardu na shedu saboda a duba a kuma dauki mataki, kamar yadda aka bukata’’ Kafin dai shi hukuncin da ba dade da yankewa ba wadda mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta yi, wanda kuma tayi amfani ne da ‘yancin da yake da shi Dasuki na dan Adam, da akwai Alkalai hudu wadanda suka yanke hukunci na a sake shi ta hanyar bashi beli, kuma Alkalai ne na babbar kotu, wadanda suka hada da maishari’a , mai shari’a Ahmed Muhammed, na babbar kotun tarayya ta Abuja, da kuma maishari’a Hussein Baba – Yusuf da Peter Affen na babbar kotu ta babban birnin tarayya. Sai kuma kotun adalci ta kasashen kawancen tattalin arziki na kasashen yammacin Afirka, ita ma tayi kira da a sake shi daga tsaron da ake ma shi. Akwai dai abokai, masoyan shi, har ma da yi ma shi fatan alkhairi, sun garzaya gidan shi, tun karfe takwas na safe, saboda suna sa ran gwamnatin taraytya zata sake shi.
Daga LeaderShip Hausa
No comments