Ya Zama Dole Saraki Ya Fadi Inda Ya Dosa – APC
Ya zama tilas shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya bayyana mana in har yanzun yana cikin Jam’iyyar APC ne ko kuma shi ma ya fice, mataimakin sakataren yada labaran Jam’iyyar na kasa, Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya.
Nabena ya ce, ya fito ya shaida manan ya zama tilas, domin duk wasu makusantansa da suka hada da, Alhaji Abubakar Kawu Baraje da shugaban ma’aikatan ofishinsa, Dakta Hakeem Baba Ahmed, duk sun fice daga cikin Jam’iyyar ta APC.
“A ‘yan kwanakin nan, akwai wani yunkuri da wasu hadakan macuta daga ciki da wajen Jam’iyyar namu ta APC, suka yi na ganin sun tozarta Jam’iyyar da kuma gwamnatin tarayya. Shugaban Majalisar Dattawan, Dakta Bukola Saraki, ya boye a cikin makarkashiyarsa.
Saraki bai taba boye tausayawarsa ba ga wadanda ke kokarin yi wa Jam’iyyar zagon kasa, wacce daga shi kansa har su din duk ita ce ta kai su matsayin da suke a kai a halin yanzun” In ji sanarwar
No comments