AdSense

Zaben Ekiti 2018: Koh Ya Za’a Kare?

Gobe Asabar za a yi ta ta kare a zaben Gwamnan Jihar Ekiti, inda ake sa ran manyan jam’iyyun kasar nan biyu APC da PDP za su gwada kwanji. Tuni Hukumar Zabe ta kasa INEC ta shirya don gudanar da zaben, wanda yake haifar da zaman dar-dar, sakamakon zafin adawar da aka yi fama da shi a lokacin yakin neman zabe da damuwar da al’ummar jihar suka nuna na yiwuwar rigingimun siyasa da murdiyar zabe a tsakanin manyan jam’iyyun.

Jam’iyyar APC mai mulki a kasa da Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, sun yi ta musayar yawu a tsakaninnu a lokacin manyan tarurrukan yakin neman zabe da suka gudanar a jihar.

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci shugabannin Jam’iyyar APC zuwa gangamin yakin neman zabe ta ranar karshe a shekaranjiya Laraba, inda suka cika jihar domin tallata dan takarar Gwamnan APC, Kayode Fayemi.

Shugaba Buhari ya roki al’ummar jihar su kada kuri’arsu ga Fayemi, wanda ya ce yin hakan ne zai kawo musu yalwa da albarkar da za ta rika bibiyar jihar har shekaru aru-aru nan gaba.

Daga nan sai Buhari ya ce al’ummar Ekiti su yi kaffa-kaffa da masu kitsa karairayi da algungumanci a kansa, suna yi masa sharrin cewa da gangan ya bari rikicin makiyaya da manoma ya yi kamari a kasar nan.

“Suna kulla min sharri cewa wai ban yi komai a kan rikicin ba, saboda ni ma Bafulatani ne. Amma wannan sharri ne kawai. Muna yin bakin kokarinmu domin ganin an samu sahihiyar hanyar magance wadannan rikice-rikice,” inji shi.

Buhari yana mai da raddi ne kan yadda Jam’iyyar PDP ta fito ta ce ya zuba ido ana kashe dimbin rayuka, sakamakon rikice-rikicen makiyaya da manoma, ya ki yin komai.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin fuskantar zaben na gobe, inda Sakataren Aiwatarwa na Hukumar, Dokta Musliu Omoleke ya ce sun shirya don gudanar da zaben. Ya ce sun raba kayan aiki zuwa dukan kananan hukumomi 16 da ke jihar, kuma sun horar da ma’aikatan wucin-gadi sama da dubu 11 wadanda za su yi ayyukan zaben a mazabu 2,195.

Dakta Omoleke ya bukaci jama’a su zabi wanda suke so domin hukumar za ta yi sahihin zabe.

Hakazailka Shugaban ’Yan sanda na kasa, Ibrahim Idris ta bakin Kakakin Rundunar, Jimoh Moshood ya bayyana cewa, ’yan sanda ba za su mara wa kowa baya ba, za su yi aikin tabbatar da tsaro ne kawai. ’Yan sanda za su tsaya a kan gaskiya. ’Yan sanda za su kare kowa tare da kuri’unsu domin su yi tasiri a zaben.

Haka Shugaban ’Yan sandan ya sha alwashin korar duk dan sandan da aka samu ya bar aikinsa ya shiga harkar siyasa a yayin gudanar da zaben na gobe. Kawo yanzu dai an jibge jami’an’ yan sanda sama da dubu 30 a jihar ta Ekiti domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben.



No comments

Powered by Blogger.