AdSense

2019: Abunda Yasa Muka Hada Kan Mu Dan  Kau Da Buhari – Buba Galadima

Mako guda da bayyana kafa wani bangare na Jam’iyyar APC mai suna Ar-e-fisi (rAPC) da kuma yunkurin hadewar bangaren da Jam’iyyar PDP da wasu jam’iyyu don kada Buhari a zaben badi, Aminiya ta tuntubi jagoran rAPC, Injiniya Buba Galadima kan dalilinsu na kokarin kau da Shugaba Buhari daga mulki da sauran batutuwa:

Yaya aka yi kuka fara wannan tafiya ta rAPC?

Mun faro wannan tafiya ce bisa kishin kasa da sadaukarwa muka kafa Jam’iyyar APC da kyawawan manufofi ga al’ummar kasar nan musamman talakawa marasa gata. Amma mafi a’ala gaba daya shi ne kokarin tabbatar da dimokuradiyya mai inganci. Amma abin mamaki da Allah Ya ba mu mulki a APC, sai shugabanninta suka fara sakin layi, ba sa bin ka’idojin dimokuradiyya sannan ba ruwansu da duk wanda ya wahala, in dai ba ya da gata, ba ya da uwa a murhu.

A takaice wadannan ne hujjojin da suka sa muka dauki matakin kawo gyara da yardar Allah. Kuma alahamdulillahi wannan motsi da muka yi, ya girgiza kasa ya samu karbuwa ga duk mai hankali. Hatta wadanda suke zaginmu, yau sun samu martaba an san da zamansu. Shugaban kasa a da ya ce ba zai yi mu’amala da barayi ba, amma sai ga shi yau har zuwa gidajen barayi yake yana durkusawa yana neman alfarma daga gare su. Ko a nan muka tsaya, mun cimma burinmu, mun cimma nasara kan abin da muke son tabbatarwa.

To amma yanzu Buhari kuke son kayarwa ne ko APC?

Wato abin da nake so ku ’yan jarida da sauran al’ummar Najeriya su sani shi ne, Buhari fa ba ma’asumi ba ne, ba Annabi ba ne, ba kuma Allah ba ne! Kuma wannan mukami da yake rike da shi, mukami ne da duk dan Najeriya yake da dama ya nema, in an yarda da shi ana iya zabarsa, saboda haka kada ku dauka cewa baya ga Buhari babu wani mutum. Tun kafin Buhari ya yi Shugaban kasa wadansu sun yi, na sojan da na farar hula. Kuma a bayan Buhari za a yi wadansu idan muna da rai da lafiya. Abin da muka ce shi ne muna son kawo gyara ne cikin jam’iyyarmu, wacce muka sadaukar muka gina.

Injiniya an ruwaito cewa kun ce ba za ku bar APC ba, amma sai ga shi kun kulla kawance da PDP da wasu jam’iyyu, me hakan ke nufi?

Mu duk wanda ya yarda da ra’ayinmu, to abokin tafiya ne. Idan APC ta ce ba ta yarda ta kawo gyara dan Adam ya zama yana da muhimmanci a tafiyarta ba, ai ba dole ba ne. Dimokuradiyya muke yi, idan Fir’auna ko Shaidan za su tuba kuma su gyara, to me zai hana mu yi tafiya da su don taimaka wa al’ummarmu?

Ka ce Oshiomhole ya tafi kotu idan bai gamsu da zamanka shugaban jam’iyya ba, me kake nufi?

Abin da nake nufi a sarari yake, sharadin dimokuradiyya ke nan! Ai ba mulkin dabbobi ake yi ba, kuma ba zai yiwu don kawai wani na rike da wani mukami na siyasa a ce abin da ya ga dama zai yi ba. daya daga cikin sharuddanmu shi ne dukanmu dole ne mu yarda ba mu da alkali sai shari’a, kowa aka yi masa abin da bai ji dadi ba, to ya tafi kotu, kuma shi ne kawai kundin mulkin Najeriya ya yarda cewa zai iya shiga tsakani ya tsage gaskiya. Don haka in shi zai tafi kotu ba mu iya hana shi, shi ma ba shi iya hana mu zuwa kotu.Da ai cewa ya yi ma zai kakkarya mu, mu ba mu isaba, amma sai ga shi yana guje-guje, ya je gidan wannan yau gobe ya je gidan wancan. Wanda a da ba su dauke shi da daraja ba, yau suna kiransa.

Wadanne nasarori motsinku ya cimma?

Da can sun mai da kowa ba kowa ba, kamar Allah ne Ya aiko su, kuma kuri’ar talaka tana aljihunsu babu wanda ya isa, amma ga shi suna zuwa gidajen wadanda suke kira barayi, ai ko yanzu mun ci nasara, kuma mun cimma buri. Kuma sun san mun isa, za mu iya hana su barci, muna iya aikawa da su gidan yari idan sun fadi a zabe. Yanzu shi Oshiomhole zai iya yin bayanin yadda ya samu gidajensa a nan Abuja da can garinsu Benin? Ina ne gonar mahifinsa ko kakansa wadda ya yi noma ya samu?

Ke nan wannan na cikin korafe-korafenku?

Ai nasara ka tambaye ni wannan ba nasara ba ce? Sannan irin sakonnin da muke samu na goyon baya daga kasar nan da wasu kasashen waje da shugabannin kasashe ma, wallahi kai in na gaya ma, kana iya gaya wa Buhari don Allah kada ya tsaya zabe.

Wadanne kasashe ne?

Don me zan gaya maka?

Don al’ummar Najeriya su sani.

To ba yanzu ba, sai nan gaba.

Mutane na ganin cewa wannan tafiya ta ’yan sabuwar PDP ce ka hada kai da su. Amma har yanzu ba ga irin su Saraki da Dogara da ba, me za ka ce?

Tambayar da zan yi maka! Kai a iya saninka wane ne mai gidana a siyasa?  

Shugaba Buhari.

To ka je ka gaya wa Buhari shi ba mai gidana ba ne, shi abokin tafiyata ce, ni ba yaronsa ba ne. Ya taba biyana albashi?  

Amma ai ka taba zama Sakataren jam’iyyarsa ta CPC…

Ba jam’iyyarsa ba ce ka je ka tamabaya!Ba shi ya kafa CPC ba, gara ku kiyaye wannan musamman ku ’yan jarida. Ni da Sule Yahaya Hamma muka kafa CPC, ya zo ya shiga. Idan ba ku sani ba ku je ku bincika. Kuma abin da kuka kasa fahimta ko in ce duk al’ummar Arewa suka kasa fahimta, Buhari fa rabonmu yake ci, mulkin nan namu ne, amma da ya hau ya yi kane-kane ya hana kowa motsi, amma duk da haka ana ganinsa mai gaskiya.To dole sai al’umma sun farka, domin mu ’yan Arewa da muka zabe bai yi mana komai ba har yanzu. Sai karkashe mu da ake yi, amma kuna ta yi masa tafi.

Wa kuke muradin ya kara da Shugaba Buhari a 2019?

Ai kai mai hankali ne kuma dan Najeriya. Kai ba ka san mutumin da ya cancanta ya shugabanci Najeriya ba sai wani ya gaya maka.

Mene ne sakonka ga al’ummar Najeriya?

Sakona gare su shi ne koyaushe kada su dubi wanda yake magana, su dubi maganar. Kuma abin da muke fada ba yau muka fara ba. Tun daga 1998 har zuwa yau, babu abin da na fada game da siyasar kasar nan da bai tabbata ba. Don haka abin da nake cewa al’ummar Najeriya shi ne su duba shin ana yi musu adalci a wannan mulkin ko ba a yi musu. Su ne alkalan kansu.

 



No comments

Powered by Blogger.