AdSense

Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin APC Da r-APC

Rikicin da ke tsakanin Jam’iyyar APC mai mulki a karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole da wadanda suka balle suka kafa Ar-e-fi-si (rAPC) a karkashin jagorancin Injiniya Buba Galadima ya dauki sabon salo bayan da Buba Galadima ya nemi Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ki amincewa da sababbin shugabannin Jam’iyyar APC na kasa.

Wannan salo ga dukan alamu yana iya kai bangarorin biyu ga gurfana a gaban kotu don warware wannan takaddama.

Injiniya Buba Galadima wanda ya jagoranci wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC suka hada da mambobin tsofaffin jam’iyyun CPC da CAN da ANPP da wani bangare na APGA, sun balle ne a ranar 5 ga Yuli nan.

An rika tunanin ko sun bar Jam’iyyar APC din ce gaba daya, ganin bayan kwanaki kadan da bayyana kafuwar Ar-e-fi-sin din sun je sun saka hannu kan yarjejeniya da Jam’iyyar PDP da wasu jam’iyyu 38 don hada karfi da karfe su yaki Shugaba Buhari a zaben badi.

Sai dai ana cikin wannan tunani ne sai ga Buba Galadima ya ruga Hukumar Zabe ta kasa (INEC) inda ya bukaci Shugabanta Farfesa Mahmoud Yakubu ya janye amincewar da suka yi da zaben shugabannin Jam’iyyar APC na kasa na ranar 23 ga Yuni bana.

Injiniya Buba Galadima ya ce zaben da aka yi a filin Eagle Skuare da ke Abuja ya saba tsarin mulkin Najeriya da na Jam’iyyar APC da Dokar Zabe.

A cewarsa zabubbukan da aka yi a mazabu da kananan hukumomi da jihohi a ranakun 2 da 5 da 8 ga Mayun bana, duk ya kamata a rusa su domin a cewarsa an samu matsaloli a jihohi 22 inda aka zabi shugabanni kashi biyu.

Ya lissafo jihohin da cewa sun hada da  Abiya da Adamawa da Bauchi da Benuwai da Kuro Riba da Delta da Enugu da Imo da Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da Kebbi da Kogi da Kwara, da Legas da Neja da Ondo da Oyo da Ribas da Sakkwato da kuma Zamfara.

“Wannan abu da ya faru ya saba wa doka ta 20(1) na tsarin mulkin Jam’iyyar APC,” inji shi.

Ya ce zaben ya yi karan-tsaye ga Sashi na 223 (1) da (2) na tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda ya ce tilas ne ga jam’iyun siyasa su yi zabubbuka lokaci zuwa lokaci. “Amma su Kwamared Adams Oshiomhole da Shugaba Muhammadu Buhari ba zabe suka yi ba, sun taru ne sun mika mulki ga wadanda suke so kawai,” in ji shi.

Sai dai tun kafii Buba Galadima ya je hukumar zaben, Jam’iyyar APC a farkon wannan mako ta ce za ta kai shi da magoya bayansa gaban kuliya.

Mai bai wa Jam’iyyar ta kasa Shawara a kan Harkokin Shari’a, Barista Babatunde Ogala, ne ya bayyana haka ga manema labarai a wani sako da ya aiko wa Aminiya ta yanar gizo. Barista Ogala ya ce Injiniya Galadima da magoya bayansa sun ci zarafin Jam’iyyar APC, sun ci amanarta, kuma suna ta kokarin jawo mata bakin jini a idon ’yan Najeriya da duniya baki daya.

Kakakin Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, Mista Rotimi Oyekanmi, ya bayyana wa Aminiya cewa babu mamaki su Buba Galadima sun kai takardar korafin nasu amma shi ba ya da tabbacin haka.

Sai dai Kakakin Jam’iyyar APC ta kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce su Buba Galadima sun yi riga Malam Masallaci.

A cewarsa, abin da ya dace su yi shi ne su kai korafinsu ga kwamitin da Jam’iyyar APC ta kafa a karkashin jagorancin Sanata Adamu Aliero domin sauraron bayanin duk wanda bai gamsu da zabubbukan da aka gudanar ba.

“A hakikanin gaskiya hukumar zabe ba za ta share musu hawayensu ba,” inji Malam Bolaji Abdullahi.  Ya kara da cewa, “Hukumar zabe ’yar kallo ce kawai a zabubbukan da muka yi. Abin da ya dace su yi shi ne idan ba su gamsu da abin da Sanata Aliero zai yi ba sai su garzaya zuwa kotu.”

Tuni masana shari’a suka sha bamban kan wannan gumurzu da ke tsakanin bangaren su Buba Galadima da Kwamared Adams Oshiomhole.

Dokta Biodun Layonu (SAN) cewa ya yi su Buba Galadima aikin banza kawai suke yi.

“A ganina burinsu shi ne su wargaza Jam’iyyar APC sannan su yi gaba; yaya za su ce sun kafa tasu jam’iyyar sannan kuma su ci gaba da damun tsohuwar jam’iyyar da suka bari? Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa damar kafa jam’iyyarsa. Abin da ya dace shi ne tunda sun tafi, to su kyale wadanda suke cikin APC su ci gaba da hidimominsu,” inji shi.

Amma Mike Ozekhome (SAN) cewa ya yi ’yan Ar-e-fi-si (rAPC) suna da hurumin da hukumar zabe za ta amince da su somin zabubbukan da aka yi a baya a jihohi suna tattare da matsaloli.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa dai suna zargin cewa wadansu manyan ’yan siyasa ne a Majalisar Dokoki ta kasa suke tunzura su Injiniya Buba Galadima domin su wargaza Jam’iyyar APC.



No comments

Powered by Blogger.