Chelsea Za Ta Yiwa Liverpool Katsalandan Wajen Daukar Alisson
Chelsea na shirin shammatar Liverpool wajen daukar mai tsaron raga Allison, in ji jaridar Mirror.
Kamar yadda aka ruwaito a baya cewa Liverpool ta fara tattaunawa da Roma kan batun mika tayin fan miliyan £62 don daukar mai tsaron ragar mai shekaru 25.
Sai dai kuma yanzu Chelsea ta shirya mika tayin fan miliyan £70 a yunkurin da take na ganin ta sha gaban abokiyar hamayyarta a gasar Premier League wajen daukar mai tsaron ragar dan kasar Brazil.
No comments