Zidane Zai Koma Juventus A Matsayin Mai Ba Da Shawara
Tsohon mai horar da Real Madrid Zinedine Zidane zai koma Juventus a matsayin mai ba da shawara, a cewar Libertad Digital.
Zidane ya yi murabus mai cike da ba zata a matsayin mai horar da Madrid a watan Yuni bayan nasarar lashe gasar Zakarun Nahiyar Turai karo na uku a jere.
Bafarenshen zai koma tsohuwar kungiyar da ya taka wa leda daga shekarar 1996-2001.
No comments