An Bawa Chelsea Damar Sake Daukar Cech
Arsenal ta bawa Chelsea damar sake daukar mai tsaron raga Petr Cech, a cewar jaridar Daily Mail.
Cech ya shafe tsawon kakar wasa 11 a Chelsea kafin ya koma Gunners, wadda yanzu ke neman hada kudaden da za ta shiga kasuwar hada-hadar yan wasa dake ci a wannan lokacin don yin cefanen yan wasa.
Ana tsamanin Blues din za ta rasa Mai tsaron raga Thibaut Courtois a wannan kakar, sannan kuma ana hasashen cewa Gunners na son maye gurbin Cech da Kasper Schmeichel ko Gianlugui Donnarumma.
No comments