Hako danyen mai ya ragu-Ma’aikatar Man Fetur
Wata kididdiga da ma’aikatar albarkatun man fetur ta fitar ta nuna cewa albarkatun danyen man fetur na Najeriya ya ci gaba da kasancewa kasa da yadda aka yi hasashe a kasafin kudi na shekarar 2018 a cikin watanni biyu.
A kasidar da ma’aikatar albarkatun man fetur ta raba wa manema labarai jiya ta nuna cewa aikin samar da danyen man ya tsaya a ganga miliyan daya da digo 82 a watan Mayu da kuma ganga miliyan daya da digo 89 a watan Yuni a shekarar 2018.
Hakan ya yi kasa da ganga miliyan biyu a rana na danyen man wanda kasar ta cimma a watanni hudu na shekarar 2018 kuma ya yi kasa da ganga ,miliyan biyu da digo uku da aka kabe a kasafin kudin shekarar 2018.
Kasidar wacce ma’aikatar ke bayyanawa duniya harkokin da suka danganci mai da iskar gas na Najeriya ta nuna cewa mafi kololuwar aikin samar da danyen mai da ta gudanar a tsakanin watan Janairu da Afrilu ganga miliyan biyu ta iya fitarwa a rana ban da watan Fabarairu inda ta hako ganga miliyan biyu da digo daya a rana.
No comments