Kalaman Obasanjo: Babu gaskiya A Cikin Ta – Lai Mohammed
Ministan Yada Labarai Lai Mohammad ya mayar da martini bisa kalaman Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo inda ya zargi gwamnatin Shugaba Buhari shirin daure shi.
A cewar Lai Mohammed, “Mara laifi ba ya tsoro domin masu laifi ne kawai ya kamata su rika jin tsoro.
“Muna mayar da hankali ne bisa gyara barnar da PDP ta yin a tsawon shekara 16, don haka gwamnatin Buhari ba za ta damu da wasu zarge-zargen da ba su da ma’ana ba,” inji Lai.
No comments