AdSense

Buhari na shirin kulla min sharri- Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya zargin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shirin daure shi saboda sukar gwamnatinsa da ya yi.

A cewar Obasanjo, “Na samu labari daga wasu majiyoyi na tsaro inda suka tabbatar min da cewa gwamnati na shirin amfani da hukumar EFCC da wasu shaidun zur domin a daure ni.”

Wannan bayanin na kunshe a wata takarda wadda mai magana da yawun tsohon shugaban Mista Kehinde Akinyemi ya sa wa hannu, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar nan suka wallafa.



No comments

Powered by Blogger.