Rochas Okorocha Zai Tsaya Takarar Sanata a 2019
Gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyan aniyar sa ta tsayawa takarar sanata a 2019, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin Orlu Zone Political Leaders lokacin ziyarar da suka kai masa a gidan gwamnatin, Owerri, inda suke kiran shi da ya tsaya takarar ta sanata.
Rochas zai tsaya takarar ne a karkashin jamiyyar APC, Inda hakan yayiwa al’umar Orlu dadi bayan karbar tayin da suka kai masa
Dr. Steve Orji, Shugaban yankin Orlu, ya fadi hujjojin su na neman ya tsaya, inda ya ce duba da yanda ya samar da cigaba a jahar Imo basu da wani zabi face ya dawo ya wakilce su a mazabar.
Rochas Ya godewa shugabanin yankin, da irin kaunar da suka nuna masa duk da shagube da yake fitowa daga yan adawar siyasa.
.
No comments