Ganduje ya bada hutun shekarar musulunci a Kano
Gwamnatin jahar Kano ta bada 11/9/2018 hutun sabuwar shekara musulunci wanda yayi dai-dai da 1/1/1440 AH Muharram
Sanarwar ta fito ne daga kwamishinan yada labarai na jahar Kano Muhammad Garba a yau litinin 10 ga watan na Satumba.
Kamar yadda sanarwar ta nuna, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya taya dukkan al’ummar musulmai murna da farin cikin shigowa sabuwar shekarar ta musulunci, ya kuma kara da cewa dukkan wani ma’aikacin gwamnati ya tsaya tsayin daka da kara kwazo cikin aikin sa dan samar da cigaba
Gwamna, Ganduje yayi kira ga dukkan yan Najeriya da su hada hannu da karfe wajan ganin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samar da cigaba da zaman lafiya da jituwa a cikin al’umma.
No comments