AdSense

Nine Kadai Zan Iya Kada Shugaba Buhari- Kwankwaso

Tsohon gwamnan jahar kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya bayana cewa shi ne kadai dan takarar da zai iya kada shugaban kasa Muhammada Buhari,

Don haka yafi son ayi zaben fidda gwani maimakon gayon bayan wani dan takara kai tsaye

Kwankwaso ya bijircewa kudurin kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP na tsayar da dan takara da kuma kokarin bawa Arewa ta tsakiya takarar shugaban kasar

A tattaunawar da jaridar NAN tayi da Binta Sipikin, mai Magana da yawun kwankwaso, ta bayyana cewa,  “abu mafi mahimmance a PDP shine jam’iyyar ta tsayar da mutun daya wanda zai iya kada shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda wannan mutum shine Kwankwaso idan ana maganar dunbun mai goyan bayan mutane’’

Shin ko meye dalilin kwankwaso na kin amincewa da yin mubaya’a ga dan takara, tace Kwankwaso mutum ne daya aminta da dokokin tsarin da jam’iyar ke tafiya akai, don haka yake so ayi zaben na fidda gwani kuma zai bada gudunmawa dari bisa dari don ganin jam’iyar ta lashe zaben  na 2019



No comments

Powered by Blogger.