Kano Pillars Za Ta Buga Wasan Sada Zumunta Da Gombe United
A wani bangare na yunkurin da suke na ganin sun lashe gasar Kwallon Kafa Ajin Kwarraru ta Nigeria, Masu Gida za su fafata da Gombe United a wasan sada zumunci.
Zakarar gasar ta Nigeria har karo hudu zata kara da Gombe United bayan dawowa daga hutun Kofin Duniya, kamar yadda jami’an kungiyar suka sanar.
Kungiyar na fafutukar ganin ta dare mataki na daya a gasar wanda zai ba ta damar cikar burinta na lashe gasar ta kwallon kafa ajin kwarraru ta Nigeria.
Kungiyar bata yi rashin nasara ba cikin wasanni 7 da ta buga gabanin tafiya hutun gasar Kofin Duniya. A halin yanzu kungiyar na a matsayi na uku da maki 38.
Kakakin kungiyar Idris Malikawa ya ba tabbacin cewa za a buga wasan ranar Asabar 14 ga watan Yuli a Sitadiya din Sani Abacha dake Kofar Mata.
Mai horar da kungiyar, Ibrahim Musa zai yi amfani da wasan sada zumuncin a matsayin zakaran gwajin dafin shirin tunkarar karawa da El-Kanemi a mako na sama, kafin daga bisani kungiyar ta sake fafatawa da zakarar gasar Plateau United.
No comments