AdSense

Dan Wasan Lobi Star Anthony Okpotu Ya Koma Difaa El-Jadida

Kungiyar Lobi Star da ke buga gasar kwallon kafa ajin kwarraru ta Najerita ta ba da tabbaci a shafinta na zumunta na Twitter ranar Alhamis cewa Dan wasan gaban kungiyar Anthony Akpotu ya koma kungiyar Difaa El-Jarida da ke kasar Morocco.

Dan wasan mai shekaru 24 ya yi nasarar jefa kwallaye 19 a raga a kakar wasa ta bara a gasar kwallon kafa ajin kwarraru ta Najeriya. Wanda hakan ya ja hankalin mai horarwa Salisu Yusuf ya saka sunansa cikin tawagar yan wasan suka wakilci kasar Najeriya  a gasar African Nations Championship a farkon shekarar da mu ke ciki.

Ya yi nasarar jefa kwallaye biyu a raga a gasar da yan wasan Najeriya masu taka leda a cikin gida suka kare a matsayi na biyu bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Morocco a wasan karshe na gasar.



No comments

Powered by Blogger.