AdSense

Majalisa Ta Amince Da Kasafin Kudin Bana

A jiya ne  16 ga watan mayu Majalsar Dattawa da amince da kasafin kudin bana na kimanin Naira triliyan 9.120.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da kasafin kudin a gaban majalisar tun a watan Disambar bara, inda ya kaddamar da kasafin Naira triliyan 8.612, amma kuma majalisar ta kara kasafin kudin zuwa Naira triliyan 9.120.

Majalisar ta amince da kasafin kudin ne bayan shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Sanata Danjuma Goge ya gabatar da rahotonsa.



from Oak TV Hausa https://ift.tt/2IyoJ9W
via IFTTT

No comments

Powered by Blogger.