AdSense

Dara Ta Ci Gida: Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Kanshi A Borno

A jiya ne Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Shiyyar Jihar Borno ta fid da sanarwar cewa wani dan kunar bakin wake ya halaka kansa da bam a yayin da hakarsa ta ki cimma ruwa na kai mummunan hari a kasuwa.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Borno, Damian Chukwu ne ya tabbatar da afkuwar wannan lamari a wata takardar manema labarai da ya fitar a garin Maiduguri, inda ya shelanta cewa, lamarin ya faru ne a daren Asabar da misalin karfe 7:20 a Kasuwar Monday.

Kwamishinan ya bayyana cewa, dan kunar bakin waken da ake zargin dan Boko Haram ne ya yi niyyar kai mummunan farmakin ne a kasuwar Monday inda al’umma ke hada-hadar kasuwanci cikin dare.

“Dan Kunar bakin waken na miji ne, wanda bayan da ya lura da irin tsaron da kasuwar take da shi, sai ya tayar da kanshi, inda ya kashe kanshi shi kadai. “Mun kara yawan ‘yan sanda a sassa daban-daban na jihar, ciki har da babban birnin jihar don bayar da tsaro ga al’umma. Kuma mun yi haka ne domin tabbatar da kiyaye rayuwa da dukiyar al’umma ganin cewa bukukuwan sallah sun gabato.” inji shi



No comments

Powered by Blogger.