RIKICIN JIHAR FILATO: Janar Tukur Yusuf Buratai Ya Fasa Kwai......
... Akwai hannun manya ko dattawan jihar Filato a cikin rikicin jihar - Buratai
Daga Haji Shehu
Babban hafsan sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewar akwai hujjoji karfafa dake tabbatar da Kungiyoyin ta'addanci na kabilu a jihar Filato wanda manyan mutane ko dattawan jihar ke daukar nauyin su.
Buratai ya baiyana haka ne jiya lokacin da ake bison gawar wasu sojoji guda 3 wadanda aka kashe a rikicin daya barke a ranar 6 ga watan Satumba a karamar hukumar Barkin Ladi.
Komandan rundunar "Operation Safe Haven", Major-General Augustine Agundu, shi ya wakilci Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai yayin bison Sojojin wanda ya gudana a barikin Rukuba.
No comments