AdSense

Nigeria Za Ta Lashe Kofin Duniya A Kasar Mexico A Wata Mai Zuwa

Mai horar kungiyar kwallon kafa ta masu fama da nakasa ta Najeriya, Victor Nwenwe, ya bayyana kwarin gwiwar tawagarsa ta ‘Special Eagles’ za ta nuna bajinta a gasar da zata halarta a kasar Mexico.

Kociyan, wanda ya bayyana alwashin tawagar yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, ya ce yanzu haka ‘yan wasan na Najeriya wato Special Eagles sun dukufa wajen atisaye a Legas domin tunkarar wannan gasa.
A ranar 24 ga watan Oktoba da muke ciki, za’a soma gasar cin kofin duniya na kwallon kafar masu fama da nakasa, wadda zata kare a ranar 5 ga watan Nuwamba a kasar Mexico dake kudancin Amurka.

Najeriya dai na rukuni na 5, tare da kasashen Rasha da Brazil da kuma El Salbador kuma zata fara buga wasanta na farko da kasar Rasha sai kuma wasa na biyu da Brazil kafin kuma ta buga wasa na uku da kasar El-Salbador.
“Mun shirya lashe wannan gasar saboda mun fito da kwariimu kuma zamuyi duk iya yadda zamuyi domin ganin mun bawa duniya mamaki a wannan gasar” In ji kociyan ‘yan wasan

No comments

Powered by Blogger.