AdSense

Pogba na son taka leda a karkashin Zidane

Alhaji Paul Pogba ya zaku da ya taka leda a karkashin mutumin da ya ke dauka a matsayin gwarzon shi wato Zinadine Zidane, sa’ad da rahotanni ke nuni da cewa Manchester United za ta kwankwasawa tsohon kocin na Real Madrid kofa don maye gurbin Jose Mourinho, a cewar Metro.

Batun tsamin dangantaka tsakanin Bafaranshen da Mourinho abu ne da aka tabbatar da shi, kuma an ce dan wasan ya fadawa mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodwork cewa yana son barin Old Trafford lokacin da za a bude kasuwar musayar yan wasa a watan Janairu.( kuma tuni aka jiyo Suarez na cewa zaiyi marhabun da zuwan Pogba Barcelona)

Alhaji Paul ka iya sauya tunaninsa na barin Old Trafford muddin aka sami sauyi a kungiyar. Duk da shike Manchester United ta musanta tattauna batun maye gurbin Mourinho, batun sallamar dan kasar Portugal din da maye gurbinsa da Zidane na ci gaba da zama abinda ake ta tattaunawa akai cikin makwanni. Yayin da aka jiyo jaridar Sun na cewa “Paul Pogba ya tashi da son Zidane a matsayin tauraronsa,kuma zai so ya taka leda a karkashinsa.”



No comments

Powered by Blogger.