AdSense

Dama Mata Zasu Karanta Wannan Gajeren Tarihin Na Nana Fatima (RA)



Manzon Allah (Saww) ya ce, Fatima Shugabar mataye ce baki daya. Sai aka tambaye shi, Ya Manzon Allah (Saww) ita Kuma Nana Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” Shin ko kun san dalilin da yasa ta samu irin wannan babban matsayi da girma?

An ruwaito hadisi daga Jabir bin Abdullahi Al’ansari (RA) ya ce; Mun yi Sallar Asar tare da Manzon Allah (Saww), bayan Mun idar da Sallah muna zaune tare da Manzon Allah (Saww), sai ga wani Dattijo ya zo Kai tsaye sai ya je wajen Manzon Allah (Saww) tare da yi masa bayanin halin da yake ciki na kuncin rayuwa na rashin abinci da tufafi da kuma kudi.

Sai Manzon Allah (saww) ya ce masa; “Ga shi kuwa ba ni da wani abu da zan ba ka” Sai ya ce masa; “Amma Ka tafi gidan Fatima”. 

Wannan Dattijo sai ya kama hanya zuwa gidan Sayyida Fatima (RA) da ya je gidan ya yi sallama.

Bayan haka ya shida wa Sayyida Fatima (RA) ga halin da yake ciki na rashin abinci da tufafi da kuma kuddi.

A lokacin da ya zo Nana Fatima ita ma ba ta da shi, saboda haka sai ta je ta dauko shimfidar 'ya'yanta (Wato Hasan da Husain), ta ce ga shi ya je ya sayar domin ya biya bukatarsa.

Sai Dattijon ya ce shi ba zai amsa ba, domin shi a tunaninsa wannan shinfidar ba zatayi kima ba. Kasancewae ya raina wannan abin da aka ba shi, sai Nana Fatima ta shiga gida ta debe abin wuyanta, wato sarka, ta kawo masa.

Sai ya amsa, bai tsaya ko’ina ba sai wajen Manzon Allah (Saww), ya same shi yana zaune tare da Sahabbai, ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) Fatima ta ba ni
wannan sarkar a kan in sayar domin in biya bukatuna”.

Nan da nan Sai Manzon Allah (Saww) ya fashe da kuka, ya ce yaya ko ba za ka samu biyan bukata ba, alhali Fatima ’yar Muhammad Shugabar mataye ta ba ka.

Sai Ammar bin Yasir (RA) ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) ka ba ni izinin sayen wannan abin wuyan”. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa yana iya saye.

Sai Ammar ya tambayi wannan Dattijon a kan nawa zai sayar masa da sakar? Sai ya ce masa; “Ni dai abin da nake bukata kayan abinci da tufa ko da kuwa daya ne, da kuma Dinare, shi ma ko da daya ne da zai kai ni garinmu”.

Sai Ammar ya hada masa kayayyakin abinci da kuma tufafi da kuma dabbar da zai hau zuwa garinsu, ya kuma ba shi kudi Dinare 20.

Bayan haka sai shi Dattijon ya zo wajen Manzon Allah (Saww), sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa; “Ka samu abinci da tufan?” Sai Dattijon ya ce; “Ya
Manzon Allah (Saww) ai ni yanzu na zama mawadaci”.

Saboda farin ciki da jin dadi, kafin ya bar wajen zuwa kauyensu, sai da ya yi addu’a, ya ce; “Ya Allah! Wanda babu wani abin bauta in ba shi ba, ka ba Fatima abin da ido bai ta'ba gani ba, kuma kunne bai ta'ba ji ba”.

Bayan haka, Ammar bin Yasir daya sayi wannan sarka, ya sa mata turare na Almiski ya nade ta a wani kyalle mai kyau ya ba Bawansa ya kai wa Manzon Allah (Saww). sarkar da Bawan, duk ya ba shi.

Daya isa wajen Manzon Allah (Saww) ya fada masa sakon. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce je ka kai wa Fatima sarkar da  wannan Bawa. Ya je wajen nana Fatima ta amshi sarkar, shi kuma Bawan, ta ’yanta shi.

Lokacin da Manzon Allah (Saww) ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce; “Wannan sarka mai albarka ta biya bukatar mabukaci (wato Dattijo) ta kuma ‘yanta bawa, ta kuma koma hannun mai ita.

Bayan duk irin wannan kyauta da Nana fatima keyi Kuma bayan kasancewarta 'yar Shugaban halitta (saww), amma gidan Mijinta Sayyidina Aliyu (RA) Sai da hannunta yayi kanta akan aikin da take yi.

Nana fatima ta kasance me biyayyah Sau da kafa a gurin mijinta kuma ta kasance mai kyauta.

A rayuwar Sayyidina Aliyu (RA) yayi aure-aure amma bayan rasuwarta, ba komai ya bata wannan matsayin ba face ayukkan da take na alkheri tare da kyautatawa mijinta.

Babu shakkah ko kinada 'yar aiki yana da kyau ki ware wa kanki wani girki wanda zaki rika dafawa mijinki da kan ki domin kara daukaka darajarki a wajensa da kuma wajen Allah (swt).

Ya Allah ka karawa Nana Fatima daraja kuma ka yi jinkai ga sauran matan da suka kaikwayi halayenta.



No comments

Powered by Blogger.