Sharhin Fim Din : kula Da Lokaci
Suna: Kula Da Lokaci
Tsara Labari: Nura Mustafa Waye
Kamfani: Intishar Multimedia
Shiryawa: Umar Isah Booth Cut
Umarni: Nura Mustafa Waye
Jarumai: Adam M Adam, Maimuna Wata Yarinya, Isah Adam, Hajara usman, Garzali Miko, Sa’adatu Dalhatu, Sani Garba S.K, Hamza F.K.D. da sauransu.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Nasir (Hamza F.K.D) yana faman gudu a cikin makarantar su a gigice, a sakamakon ‘yan daban makaranta su biyu da suka biyo sa, bayan sun yi nasarar kama shi sai suka dam’ka shi ga shugaban su na ‘yan daba wanda ake kira da suna Maja (Adam M Adam) nan take Maja yasa reza ya kyakyketa fatar jikin Nasir sannan yayi masa gargadi akan zai iyayin abinda yafi haka matukar bai fita daga cikin sabgar budurwar da yake so ba. Lokacin da wannan abun ke faruwa ne sai Laura taje ta gayawa ‘kawarta cewar Maja ya illata saurayin da take so, jin hakan ne ya fusata Abida (Maimuna Wata Yarinya) taje taga Nasir a kwance cikin jini ya suma, daga nan sai ta wuce ta samu Maja a cikin abokan sa ta soma zagin sa tana cin alwashin ita bazata taba auren azzalumin mutum irin sa ba, sai da ta gama zagin sa sannan ta juya zata tafi amma sai yabi bayan ta a fusace ya rotsa mata kwalba aka. Abida ta fadi a kasa ta suma, nan Maja yaja gayyar abokan sa suka bar wajen.
Tun daga sannan ‘kawayen Abida suka ‘kara tsorata da lamarin Maja kuma suka soma addu’ar ganin silar da zata zo don kawo karshen Maja, anan ne wata kawar Abida take bawa sauran kawayen ta labarin cewa kafin bayyanar Maja an samu wani hatsabibin a cikin makarantar wanda mai suna Raba wanda shima ya fitini ‘yan matan makarantar yana yi musu fyade, har ma sanadin hakan wasu ‘yan matan idan suka ji ya kira su dakin sa suke guduwa subar makarantar gaba daya, ana cikin haka ne wata rana ya gayyaci wata budurwa zuwa dakin sa amma da tazo suka kebe a gefe sai tayi amfani da wu’ka ta yanke mishi gaban sa. Tun daga sannan aka kawo ‘karshen zaluncin Raba a cikin makarantar.
Bayan wannan ‘kawar Abida ta gama bawa sauran ‘kawayen ta labari sai suka sa a ran su cewa wata rana za’a samu sanadin da zai kawo musu ‘karshen dan daba wato Maja. Domin a yadda aka nuna duk abinda Maja yake yi da sanin shugabannin makaranta kuma ba’a yi masa hukunci akan haka. Bayan wani lokaci sai Abida ta warke daga rashin lafiyar da take yi ta dawo ta cigaba da zuwa makaranta bayan iyayen ta sun mata gargadin cewa ta daina kula duk wasu samari, domin karatu suka turo ta tayi ba soyayya ba, hakan ne yasa da ta dawo taga Nasir shima ya dawo sai ta daina kula sa, ko da ace ya kira wayar ta sam bata dagawa, duk da har zuwa sannan tana son sa amma sai ta danne zuciyar ta saboda tabi umarnin iyayen ta. Yayin da shi kuma Nasir ya tashi hankalin sa saboda ganin ta daina kula shi, har ya kira wani abokin sa ya tura shi zuwa wajen Abida don a shawo masa kan ta, amma sai abokin nasa ya’ki zuwa wajen Abida saboda tsoron kada Maja ya gan shi da ita. A wannan lokacin ne wani sabon dalibi ya bayyana a makarantar, ganin zaluncin da Maja yake yi sai hakan ya bashi mamaki har yake tambayar meyasa aka zuba masa idanu yake cin zarafin jama’a, amma sai wani abokin sa ya nuna masa kawai yaja bakin sa yayi shiru don Maja yafi ‘karfin kowa. Ana haka kuwa wata rana Maja yaga wannan sabon dalibin tare da wani abokin sa dan daba, nan take Maja ya bangaji sabon dalibin gami da yimasa gargadi akan lallai shima ya iya takun sa don ba’a kawo masa raini, tun daga sannan wannan sabon dalibin ya soma bibiyar Maja da wadanda ya zalunta don ya nemo hanyar da zai sa shawo kan matsalar dake faruwa a cikin makarantar.
A wani bangare kuma wata rana Umar yana tafiya akan mashin din sa (Garzali Miko) sai yaci karo da wasu ‘yammata su biyo suna siyayya akan hanya, tun daga sanda yaga Meenat (Sa’adatu dalhatu) sai Umar ya kamu da son ta, hakan yasa yayi ta bin su a baya har Meenat tazo gida suka rabu da ‘kawar ta, bayan ta shiga gida a tsorace tana waige-waige sai mahaifiyar ta (Hajara Usman) take tambayar ta abinda ya faru, nan ta gaya mata wanda ke bibiyar ta. Yayin da shi kuma Umar ya jima a tsaye a kofar gidan kafin daga bisani ya juya ya tafi. Bayan wani lokaci sai mahaifin Meenat ya matsa mata akan ta fito da mijin aure, hakan sai ya soma damunta amma sai ta gayawa ‘kawar ta halin da ake ciki gami da cin alwashin zata soma kula Umar kasan cewar duk sanda ta dawo daga makaranta yakan bibiye ta amma ba sa yiwa juna magana, tun daga sannan sai soyayya ta ‘kullu tsakanin Umar da Meenat. Har ma Umar ya bawa matar yayan shi labarin abinda ke faruwa, kasan cewar an nuna yana zaune ne a gidan yayan sa, da farko matar yayan sa bata so Umar ya fara soyayya ba amma ganin Meenat ta amince dashi sai ta dawo tana goyon bayan sa.
Lokacin da mahaifin Meenat yaji labarin ta samu wanda yake son ta sai ya bata umarnin ta gaya masa ya turo iyayen sa gida ayi maganar aure, bayan Meenat ta gayawa Umar sai ya tunkari yayan sa da maganar (Isah Adam) amma sai yayan nasa yayi gardama yaki amincewa saboda ganin Umar yana karatu, nan take matar sa ta goyi da bayan Umar kuma tayi masa tuni da cewar suma fa sun yi aure ne tun bai gama nasa karatun ba. Da farko yayan Umar bai amince da zuwan sa gidan iyayen Meenat ba, amma daga bisani sai ya dauki abokin sa suka je gidan don a nemawa Umar auren Meenat. Tun daga zuwan su gidan sai abokin yayan Umar ya soma kushe gidan, (Sani garba s.k) ya dinga nuna cewa taimakawa iyayen Meenat zasuyi. Bayan Mahaifin Meenat yazo wajen su yayan Umar sai Sani s.k ya soma gaya masa magana mara dadi wadda bata kamata ba, nan take Mahaifin Meenat ya fusata suka soma rigima ya nuna musu cewar don yana talaka baza’a wulakanta shi ba. Nan take rigimar ta shafi yayan Umar suka soma musayar yawu, anan aka yi baram-baram suka watse cikin rashin jin dadi ba tare da an nemawa Umar auren Meenat ba.
Hakan ne ya tashi hankalin Meenat ta soma kuka, musanman da taji mahaifin ta yasa mata doka akan kada ta sake kula Umar. Hakan yasa wata rana da suka hadu da Umar a hanya ta’ki kula shi duk da Umar din ya nuna mata bai ji dadin abinda ya faru ba domin shima yayan sa ya nuna masa yaje ya nemi wata yarinyar ya aura. Bayan Meenat ta koma gida ne sai ta zauna a kofar gida tana kuka har Mahaifin ta ya ganta, nan take ya zartar da hukuncin tura ta wajen ‘kanin sa acan garin Kaduna don ta zauna a hannun sa ta cigaba da karatu. Bayan an gama shirin tura ta Kaduna ne sai ta bar wa /kawar ta wasiyyar ta mika mata sakon gaisuwa ga Umar don tasan ba zasu sake haduwa da juna ba. Ashe shima Umar ganin ya tada hankalin sa sai yayan sa ya yanke hukuncin tura sa can garin Kaduna don ya cigaba da karatun sa acan inda wani dan uwansa shima yake karatu.
Bayan Meenat ta fara karatu a sabuwar makarantar da aka tura ta ne sai dan uwan Umar ya ganta ya kamu da son ta, a sannan ne Abida tayi masa alkawarin zata hada su saboda ta nuna masa cewa Meenat ‘yar uwar ta ce, kuma ta fada masa haka ne badon komai ba sai don saboda taimakon da yayi mata wajen kokarin sake hada soyayyar ta da nasir, domin shi ya kawo dabarar da Abida ta soma kulla soyayyar karya da Maja har ya zamo silar da suka rabu da abokan sa yayin da ita kuma ta cigaba da son Nasir a cikin zuciyar ta.
Abubuwan Birgewa:
1- An ja hankalin me kallo a farkon fim din a yayin da Maja zai zalunci Nasir.
Kurakurai:
1- Lokacin da Maja ya yanki Nasir a baya kuma ya rotsawa Abida kwalba aka, shin ina jami’an tsaron makarantar suke? Har fim din ya ‘kare ba’a ga hukumar makaranta ta dau matakin komai akan ‘yan iskan makarantar ba. Kuma ganin ba’a dau matakin komai ba hakan zai iya kashe guiwar wasu iyayen masu son tura ‘ya’yan su jami’a, don zasu ga kamar babu cikakken tsaro a cikin jami’a.
2- Jami’ar da aka nuna su Maja da sauran dalibai suna karatu ba makaranta bace a gaske, waje ne da ake tsaron dabbobin daji (zoo) Tunda ana yin fim ne don mai kallo yaga kamar abinda ke faruwa a gaske yake kallo, ya kamata a samar da ainahin jami’a ta gaske ba wai a nuna gidan zuu a matsayin jami’a ba.
3- Lokacin da Isah Adam da abokin sa suka je gidan su Meenat don nemawa dan uwan su Umar auren ta, bai kamata su tsaya a tsaye don tattauna muhimmiyar magana haka ba, koda ace ba zasu shiga daga ciki ba, to ya dace su samu waje su zauna kafin su fara tattauna maganar.
4- An nuna cewar Jami’ar da daliban fim din suke shiga don yin karatu a garin Kaduna take, amma a zahiran ce ba Kaduna bane garin Kano ne.
5- Shin a cikin Jami’ar da su Abida ke zaune ba’a yin karatu ne sai soyayya da kuma rigima? Ko sau daya ba’a nuna daliban makarantar suna tattauna maganar karatu ba. Kuma ba’a ga dalibai sun fito daga aji ko sun shiga don daukar darasi ba.
6- Fim din ya faro daga kashi na daya har zuwa kashi na hudu amma duk da haka ba’a ga cewar labarin ya ‘kare ba, shin an rasa yadda za’a ‘karasa labarin ne shi yasa aka katse shi? Idan kuma za’a yi cigaban sa ne to ya dace a karshen fim din a rubutawa me kallo hakan don ya fahimta.
7- Ba’a nuna wa me kallo ‘karshen zaluncin Maja da ya addabi daliban makarantar su ba. Kuma ba’a ga yadda ‘karshen soyyayar Abida da Nasir ta kasance ba.
Karkarewa:
Babu jigo ko kuma wani darasi da fim din ya ‘kunsa, kuma labarin bai dire har ‘karshen sa ba. Allahu a’alamu.!

No comments