AdSense

Wasan Kallon Kafa

Atletico Madrid ta lashe gasar cin kofin EUROPA

Abin da za mu iya kawo muku ke nan, Muna taya Atletico Madrid da magoya bayanta murna.

Marseille sun yi kokari, musamman wajen taka leda, da nuna kwarewa, sai dai da alamu sun yi rashin Payet, wanda ya fita tun kafin aje hutun rabin lokaci, wanda rashinsa ya nuna a fila.

Atletico ta lallasa Marseille da ci 3 da nema a wasan karshe na kofin EUROPA. Griezman ne ya zura kwallo biyu, sannan Gabi ya zura ta ukun. Wannan ne karon farko da Gabi zai zura kwallo a wannan gasar.

92: Lafare ya busa. Eh ina nufin an tashi. Atletico 3 Marseille 0.

90: Fernando Torres ya canji Griezman.

89: Goallllllll….. Gabi ya zura ta uku. Kaf! wasa ya kare. Atletico 3, Marseille 0. Saura minti daya a tashi.

88′ Correa ya yi waje inda Partey ya shigo a madadinsa.

82: Marseille ta kara samun dama, amma kash! Amavi ya zubar da damar.

79: Goallll… Kayya.. Ina ta buga ne ta fito? Ayya ta buga sandan post ne ta fito. Kai! wannan dai rashin sa’a ne.  Amma Mitroglou ya yi kokari inda ya mike sama, sannan ya buda wa kwallon kai, amma saboda rashin sa’a, sai ta buga sandan post.

78: An  N’Jie da Harnadez katin gargadi saboda sun nema tayar da zaune tsaye

75: An ba kyaftin din Marseille  Luiz Gustavo katin gargadi, amma da alamu bai gamsu da katin ba.

70: Yanzu ne Atletico suke wasa. Sun sake natsuwa suna suna tala leda. Yanzu haka hankalin Marseille a tashe yake saboda yadda suka matsa musu lamba a gida.

68: Bugun tazara a kusa gidan Marseille bayan  Gustavo ya kwada  Griezman da kasa. Sun buga amma ba ci. Har yanzu 2 da nema. Kwallon ta dawo, goall..  Ayya Madanda ya tura ta waje.

66: Ya kamata Atletico su kara natsuwa su gyara wasansu kwarai. Kamar sun fara rudewa. Suna bata kwallo cikin sauri ko sun ja  kwallon.

64: Yanzu haka kusan duk ‘yan wasan Atletico sun dawo ne sun tare a gida.

62: Hankalin ‘yan wasan Marseille kamar yana kwance ne. Har yanzu suna ta taka leda cikin natsuwa.

60: Marseille na kokari sosai, amma suna baukatar kara zafi da kaimi wajen neman zura kwallo ba taka ledar ba kawai.

57: Yanzu Atletico sun fara samun natsuwa. Ko dan sun ga sun zura kwallo biyu ne?

55: Canji a gidan Marseille: N’Jie ya canji Oocampos. Amma dai Ocampos ne ke damun masu tsaron bayan Atletico. Ko mai ya sa ya canja shi. Mai daki shi ya fi sanin inda ruwa ke zuba.

49: Goallll…. Griezman ya zura kwallo na biyu. Koke ne a wannan karon ya taimaka masa. Atletico 2 Marseille 0. Llissafi ya fara bacewa ga Marseille. Amma dai idan da rai, hausawa na cewa da rabo. Mu je zuwa.

47: An dawo hutun rabin lokaci. Da alamu Atletico da karfinsu suka dawo filin wasan nan.

46: An je hutun rabin lokaci. Atletico 1 Marseille 0

44: Griezman ya so ya tura wa Costa kwallo mai kyau. Amma kash! Sarr na kusa inda ya tare kwallon.  Dan bukulu ke nan.

42: Ocampos ya so ya yi wa  Marseille lalata amma Gimenez mai tsaron bayan  Atletico ya tare.

38: An ba mai tsaron bayan Marseille Amavi katin gargadi.

32: Lopez ya canji Payet. Gaskiya fitan Payet ba zai yi ma goyan Marseille dadi ba, amma shi ma Lopez ba kanwar lasa bane.

31: Kash! Payet zai fita a wasan. Lafiya kuwa? Ashe ya samu rauni ne. Ayyaaa.. Yana kuka. Da alamu abin ya dame shi.

27: Ocampos na tala leda yadda ya so a gidan  Atletico.

26: Tun yanzu? Golan Atletico ya fara salon cin lokaci

24: Payet ya buga bugun tazarar, amma ta yi sama. Har yanzu dai Marseille ba sa’a.

23: Katin gargadi na farko a wasan. An ba Šime Vrsaljko dan bayan Atletico kati.

21:Goalllllllll…. Griezman ya zura kwallon farko. Duk da cewa ana danna Atletico ne a wasan. Dan bayan Marseille ya yi wani kuskure mai tsada inda ya ba Griezman kyautar kwallo a kafarsa, inda shi kuma nan take bai  yi wata-wata ba ya jefa a ragar Marseille. Atletico 1 Marseille.

18: Marseille sun kai 3, Atletico kuma 1.

16: Har yanzu dai babu ci a wanna wasa. Amma kwallon ta fi yawa a tsakiyar fili. Payet na nuna kwarewa sosai a wannan wasan. Ashe shi yasa ya nada kambu. Kuma hausawa na cewwa 9 sai gwani, 10 kuma sai dan gata.

14: Atletico sun samu bugun tazara a kusa da gidan Marseille. Amma Koke ya buga kwallon ta bude da yawa.

8: Gaskiya zuwa yanzu dai Marseiile ta fi taka leda. Tana nema ta yi Atletico ba zata.

4: Saura kiris, Marseille ta samu dama mai kyau, amma kash kwallon ta yi sama da yawa. Kai! wannan asara haka? me ya kai ka irin wannan bari Thauvi?

1: An fara wasa. Marseille na suka fara. Kuma fuskar duk ‘yan wasan nan da alamu babu wasa. Kowa ya murtuke fuska, sai Payet ne kawai ya iya zuwa ya gaisa da abokinsa Griezman.

A yanzu haka sun shigo fili. Kuma gaba ake da a fara taka ledar.

 za a fafata bugun karshe na kofin EUROPA tsakanin kungiyar Marseille na Faransa da Atletico Marid na Spain.

‘Yan wasa: MARSEILLE (4-2-3-1):  Steve Mandanda; Bouna Sarr, Adil Rami, Luiz Gustavo, Jordan Amavi; Andre-Frank Zambo Anguissa, Morgan Sansone; Florian Thauvin, Dimitri Payet, Lucas Ocampos; Valere Germain.

Benchi: Hiroki Sakai, Boubacar Kamara, Rolando, Kostas Mitroglou, Clinton N’Jie, Yohann Pele, Maxime Lopez.

ATLETICO (4-4-2): Jan Oblak; Sime Vrsaljko, Jose Gimenez, Diego Godin, Lucas Hernandez; Angel Correa, Saul Niguez, Gabi, Koke; Diego Costa, Antoine Griezmann.

Benchi: Filipe Luis, Thomas Partey, Fernando Torres, Stefan Savic, Juanfran, Kevin Gameiro, Axel Werner.

Za a fara wasan ne da misalign karfe 7:45.

Daga Aminiya Hausa

 



from Oak TV Hausa https://ift.tt/2L8ublo
via IFTTT

No comments

Powered by Blogger.